Labarai
An Hori Ma’aikatan Lafiya Su Kara Kokari Wajen Rike Aikin su
Shugaban hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitoci kula da lafiya a matakin farko ta kasa Alhaji Dr Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya hori ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da dukkannin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya su rubanya kokari fuskar tabbatar da kwarewa domin inganta ayyukan kula da lafiya a Nijeriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya yi wannan kiran ne a Katsina lokacin bukin rufe taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku na wannan shekarar wanda aka shiryawa Malaman koyar da darusan kiwon lafiya a matakin farko.
Taron wanda ya samu halartan jami’an kiwon lafiya daga dukkannin jihohin yankin arewa maso yamma, yana da nufin ilimintar dasu ne kan yadda za su rungumi sabbin dabarun aiki irin na zamani dai dai da tsarin dokokin hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitocin kula da lafiya a matakin farko ta Naheriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya bayyana cewa wajibi ne dukkannin ma’aikatan hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya a matakin farko su kara zama masu kwazo tare da yin aiki da sauran dokokin aiki na fasahohin zamani domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Don haka shugaban hukumar ya sake yin kira ga malarta taron su yi amfani da abubuwan da suka koya yadda suka dace domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a Naheriya.
Maryam Idris
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
