Connect with us

Labarai

An Tabbatar Da Mutuwar Mutum Guda Tare Da Ceto Wata Mata Daga Rijiya

Published

on

Wani mummunan lamari da ya faru a rijiya ya yi sanadin mutuwar wani mutum mai suna Salisu Musa dan shekara 50 a kauyen Gora da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Kano.

 

A cewar Saminu, wanda ya rasu yana fama da matsalar tabin hankali.

 

Ya bayyana cewa, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, Salisu ya garzaya cikin daji, inda daga bisani ya fada cikin rijiya.

 

Jami’in hulda da jama’a ya yi nuni da cewa, duk da kiran da ya yi na neman agaji, babu wanda zai iya kubutar da shi har sai zuwan tawagar hukumar kashe gobara.

 

“An same shi a sume kuma daga baya aka tabbatar ya mutu”

 

“An mika gawarsa ga Sufeto Nuhu Daniel na rundunar ‘yan sandan Madobi don ci gaba da bincike”

 

Hakazalika hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu nasarar ceto wata mata mai suna Maryam Biya mai shekaru 37 da haihuwa wacce ita ma ta fada cikin rijiya da ke kan titin Faransa a karamar hukumar Fagge.

 

Ya ce, wani dan kasa, Joseph Pitter ya kai rahoton ga Babban dakin kula da kashe gobara.

 

Saminu ya jaddada cewa, da isar su, tawagar ceto ta fitar da Maryam daga rijiya da rai.

 

“Nan take aka garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin kula da lafiyarta”.

 

Ya kara da cewa daga baya an mika ta ga dan sanda Mu’azu Abdullahi na sashin ‘yan sanda na Sabon Gari.

 

Jami’in hulda da jama’a Saminu Yusif ya yabawa kokarin da kungiyoyin bayar da agajin gaggawa suka yi a wannan lamarin.

 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su dauki matakan kariya, musamman a kusa da budadden rijiyoyi, domin hana afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.

 

Khadija Aliyu

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara