Labarai
Gwamnan Kano Ya Yi Rangwamen Kashi 50 Bisa 100 Na Takin Zamani
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya raba tireloli uku uku na taki ga Kananan Hukumomin jihar 44, tare da yin rangwamen kashi hamsin bisa dari na kudaden takin ga manoma.
Kowacce tirela tana ɗauke da buhuna 600 na taki, wanda ya kai jimillar buhuna 79,200.
An kaddamar da bikin rabon takin ne a harabar kamfanin Al Yuma Fertilizer da ke karamar hukumar Madobi.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin noma wajen ci gaban jihar, inda ya ce: “Mun taru a nan ba kawai don raba buhunan taki ba, sai don tabbatar da kara inganta dogaro da kai, da habbaka tattalin arzikin.”
Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnati ta samu a fannin bunkasa noma, wadanda suka haɗa da faɗaɗa damar samar da filayen noma, da habbaka noman rani , da kuma bayar da sabbin ayyuka a kananan hukumomi 11.
Haka kuma, ya ambaci gina dam a Dansoshiya da ke karamar hukumar Kiru, domin tallafa wa aikin noma.
Ana sa ran yin rangwamen kashi hamsin bisa dari a kan takin zai ƙara samar da abinci, habaka tattalin arziki, da wadatar abincin a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rabon taki a farkon damina ya zo a kan lokaci, wanda tabbas zai amfani manoma.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
