Kasuwanci
Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Farfado Da Kasuwar Farm Centre Da Gobara Ta Lakume
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamitin musamman domin bincike da kuma kula da abubuwan da suka biyo bayan gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyin hannu da ke Farm Centre.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya gudanar da bikin kaddamarwar a madadin Gwamnan Jihar.
An dora wa kwamitin nauyin bincikar musabbabin gobarar, sanin girman asarar da aka yi da kuma bayar da shawarwari masu amfani don kauce wa kara faruwar irin wannan iftila’i.
Da yake jawabi a wurin kaddamarwar, Alhaji Umar Farouk ya jaddada muhimmancin samar da tallafi bisa gaskiyada adalci, tare da gargadin gujewa siyasantar da shirin tallafawa waɗanda abin ya shafa.
Ya bukaci mutane, kungiyoyi da dukkan ‘yan Najeriya masu kishin al’umma da ke son bayar da taimako ga ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa, da su tura tallafinsu ta hannun kwamitin ko kuma ta asusun ajiyar gwamnati na musamman da aka ware domin hakan:
Sunan Asusun: FARM CENTRE GSM MARKET FIRE INCIDENCE SUPPORT FUNDS ACCOUNT
Lambar Asusun: 1310076187
Banki: ZENITH BANK
An nadaKwamishinan Harkokin Musamman, Alhaji Nasiru Sule Garo a matsayin shugaban kwamitin, yayin da sauran mambobin kwamitin suka fito daga ma’aikatun gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa da kuma masu zaman kansu daga sashen kasuwanci.
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa waɗanda abin ya shafa da kuma sake gina kasuwar ta hanya mafi tsari.
Gwamnati ta bukaci haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin cimma wannan manufa.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai16 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
