Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kammala Aikin Tituna Da Ta Gada A Fadin Kasar Nan
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana aiki tukuru wajen kammala aikin hanyoyin da ta gada masu tsawon kilomita dubu talatin da shida a fadin Najeriya.
Minista a Ma’aikatar Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai.

Muhammad Bello Goronyo ya kara da cewa, a karkashin Shirin “Sabunta Fata” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da karin manyan ayyuka guda hudu da wasu muhimman ayyukan ci gaba da suka shafi gina ababen more rayuwa domin sauya fasalin kasa don dorewar cigaba.
Wakilin Radiyon Najeriya daga Sokoto ya bayyana cewa, cikin manyan ayyukan hanyoyi hudu da Shugaba Tinubu ya ambata, akwai hanyar gabar tekun da take da tsawon kilomita arba’in da ɗigo bakwai (40.7km) da kuma hanyar Illaila Sokoto-Badagry wadda ke da tsawon kilomita dubu ɗaya da sittin da takwas (1,068km).
Sauran hanyoyin sun hada da hanyar Transahara da ke ratsa Akwanga, Jos, da Bauchi zuwa jihar Gombe, da kuma wata hanya da ke hade jihohin Ebonyi, Benue da Nasarawa.

Goronyo ya bayyana cewa an kammala matakin farko na aikin hanyar gabar tekun Lagos zuwa Calabar.
A cewarsa, a hanlin yanzu gwamnatin ta dukufa akan aikin tagwayen hanyoyi daga Kaduna zuwa Sakkwato, wadda ke ratsa Zaria, Funtuwa, Gusau, da Talatar Mafara zuwa Sokoto.
Ministan ya bayyana cewa ana aikin hanyar Zaria zuwa Sakkwato da nagarta, wadda ake sa ran zata iya ɗorewa sama da shekaru hamsin.

Goronyo ya jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gine-ginen hanyoyin muhimmanci sosai, yana mai jaddada cewa hanyoyi da sauran ababen more rayuwa su ne ginshikan habakar tattalin arziki a kasar.
Ministan ya kara da cewa hanyoyi masu inganci su ne ginshikan ababen more rayuwa da ke ba da damar hada masana’antu da kasuwanni, da kuma saukaka jigilar kayayyaki daga wwurarenda aka samar da su zuwa ga masu amfani.
Ya kara da cewa, baya ga bangaren tattalin arziki, gina hanyoyi na da babbar fa’ida ta zamantakewa, domin yana kara hada kan al’umma da kuma saukaka samun damar kaiwa wuraren lafiya, da zuwa makarantun gwamnati da ofisoshi, da dai sauransu.
Daga Nasiru Malali
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
