Labarai
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Bada Goron Sallah Na Naira Miliyan Biyu Ga Ma’aikata
Kungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE), reshen Malam Madori, ta yaba da kokarin Shugaban Karamar Hukumar, Salisu Sani Garun-Gabas, bisa bayar da gudunmawar naira miliyan biyu domin ma’aikatan su samu damar yin bukukuwan Sallah ta cikin farin ciki.
Shugaban Kungiyar, Aminu Tafida, ne ya bayyana haka ga Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukuma, Musa Muhammad Hadejia, jim kaɗan bayan an raba kuɗaɗen ga ma’aikata.
Aminu Tafida ya bayyana cewa wannan kyauta wani bangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar ma’aikata, domin kuwa hakan zai sa su kara samun azama wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A baya, Shugaban Karamar Hukumar, Salisu Sani Garun-Gabas, ya bukaci ma’aikatan karamar hukumar da su rike aikinsu bisa gaskiya da amana.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
