Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi

Published

on

Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.

A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.

Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce mai  kishin jasa da son cigaban ilimi da hidima ga al’umma,” in ji Sakataren Gwamnati.

Haka kuma, Gwamna Namadi ya amince da naɗa Hassan Nayaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Raya Ilimi ta Jihar Jigawa (JERA).

Kafin wannan mukami, Nayaya ya kasance mukaddashin Shugaban Hukumar. Ya samu digiri a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 2000. Ya fara aiki a ma’aikatar ilimi ta Jihar Jigawa ne tun daga shekarar 1992, har ya kai matsayin Darakta a shekarar 2020,” in ji sanarwar.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen suna daga cikin kokarin Gwamna na inganta shugabanci a fannin ilimi da ci gaban al’ummar Jihar Jigawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an yi naɗin ne bisa cancanta, kwarewa da nagarta.

Yayin da ake taya sabbin shugabannin murna, ana fatan za su yi aiki tukuru domin ba da gudunmawa ga ci gaban Jihar Jigawa.”

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara