Labarai
NAHCON Za Ta Fara Jigilar Alhazai Ranar 5 Ga Watan Mayun 2025
Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta fitar da sunayen kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar Alhazan bana.
Bayanin ya ƙunshi sunayen jiragen da kuma adadin mahajjatan da aka ware wa kowannensu.
Kamfanin Fly Nas zai yi jigilar Alhazai 22,893, kashi 32.12 bisa dari kenan na maniyyatan Najeriya a bana, yayin da Kamfanin Air peace ya sami Alhazai 9,145 , kashi 12.83.
Sauran su ne Max Air Ltd da aka warewa Alhazai 23,343, kashin 32.75 kenan bisa dari, sai kamfanin Umza Air Ltd an ware da ya sami 15,893 wato kashi 22.30 bisa 100, wanda ya kawo adadin maniyyata 71,274 da ake sa ran za su sauke farali a bana.
Hukumar ta NAHCON ta ce za a fara jigilar maniyyatan ne a ranar 5 ga Mayun 2025.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
