Labarai
Wani Bawan Allah Ya Ɗauki Nauyin Ciyar Da Masu Azumi A Kano
Wani mai taimakon al’umma a Kano ya fara gudanar da ayyukan jin kai ta hanyar bayar da abincin buda baki na azumin Ramadan kyauta ga marasa galihu a cibiyoyi goma a fadin jihar.
Ana raba Shinkafa da Kunun Tsamiya da taliyar yara, da dai sauran abinci, domin buda baki.
An kaddamar da wannan tallafin ne a daya daga cikin cibiyoyin ciyar da abinci da aka ware a garin Rimin-Gado ta hannun Barista Muhuyi Magaji.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga sassa daban-daban na jihar, sun kuma nuna jin dadinsu da wannan tallafi.
Baya ga bayar da abincin buda bakin, wannan bawan Allah ya kuma raba kayan abinci da suka hada da shinkafa da taliyar yara, da tsabar kudi ga marasa galihu sama da 2,000 da marayu 150 don tallafa musu a cikin wannan wata mai alfarma.
Mai bada agajin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an yi hakan ne don neman yardar Allah, wanda ya umarci masu imani da su ciyar da marasa galihu musamman cikin watan Ramadan.
Wadanda suka ci gajiyar shirin da suka hada da Maijidda Iro da Sadiya Yusuf sun godewa masu taimakon bisa wannan karimcin da suka ce zai ci gaba da ciyar da su a cikin wannan watan na Ramadan.
Sun yi addu’ar Allah Ya mishi sakayya da mafificin alkhairi.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
