Labarai
Shugaba Tinubu Ya Karbi Bukuncin Takwaransa Na Saliyo
A yau Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin takwaransa na Saliyo, Julius Maada Bio a fadar gwamnati da ke Abuja.
Da isarsa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya tarbe shi, kafin ya kai ziyarar ban girma da shugaba Tinubu, wanda kuma ke rike da mukamin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.
Wakilin gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa shugabannin biyu sun yi ganawar sirri, duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar da suka yi ba.
Wannan ita ce ziyarar girmamawa ta farko da Shugaba Bio ya kai wa Shugaba Tinubu. Duk da haka, ya kasance cikin mahalarta taron ECOWAS da aka rika gudanar a Abuja karkashin jagorancin Najeriya.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
