Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da N1.5 Biliyan Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa.

Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.

A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar.

Ya ce, majalisar ta kuma amince da kashe sama da naira biliyan takwas da miliyan dari biyu a matsayin kashi 30 bisa  na kudaden shirin noman rani na shinkafa na shekarar 2025.

Ya kuma yi bayanin cewa, an  amince da hakan  ne da nufin samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar miliyoyin al’ummar  Jigawa ta hanyar bai wa Manoma 58,500 rance, don noma hekta 50,000 na shinkafa a fadin yankunan da ake noman shinkafa,  kamar yadda ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta gabatar.

Kwamishinan ya ce, majalisar zartaswa ta jihar ta kuma amince da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita wa’adin shekaru 2 tsakanin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar Jigawa da kungiya mai zaman kanta ta Medicins San Frontiers (MSF)  da ke kasar Faransa.

A cewarsa, rattaba hannu kan yarjejeniyar na da nufin karfafa kokarin jihar na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ta hanyar samar da ingantacciyar kula ga masu juna biyu a babban asibitin Jahun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Miga da Ajura.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara