Connect with us

Labarai

An Bukaci Gwamnoni Su Yi Koyi Da Gwamnatin Neja Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya

Published

on

An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa  tare da tabbatar da lakabin gargajiya ga wasu fitattun Fulani guda biyu a jihar Neja, da aka gudanar a fadar Sarkin Minna.

Dokta Baba Usman Ngelzarman ya bayyana cewa, hanyar da Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ya bi na samar da sakamako mai kyau, ta yadda za a rage yawan rikicin makiyaya da manoma a jihar abin a yaba ne matuka.

A cewarsa hakan ya sanya bangarorin 2 sun kara fahimta da mutunta juna, wanda ya haifar da karuwar kudaden shiga a jihar da ma Najeriya baki daya.

Mai martaba Sarkin Minna Dr Umar Faruk Bahago, ya jaddada bukatar masu rike da mukaman gargajiya a yankinsa su rika gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah,  ta hanyar yin adalci ga kowa, don samun nasara.

A nasa jawabin sabon Jauro Minna kuma Kwamishinan kula da harkokin Makiyaya da kiwo na jihar Neja, Umar Ahmed Rebe ya yi alkawarin kara himma wajen inganta alakar manoma da makiyaya, wadda  za ta ci gaba da  kasancewa cikin kwanciyar hankali da walwala domin samun kyakkyawan sakamako.

A nashi jawabin, Wakilin Fulanin Minna, Alhaji Hassan Usman Shiroro, ya yi kira ga Fulanin jihar Neja da su ci gaba da zama lafiya da kowa domin bunkasa ci gaban jihar Neja cikin hanzari, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne abin da ake bukata na duk wani ci gaba mai ma’ana.

Daga Aliyu Lawal

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara