Connect with us

Labarai

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Ta Soki Matakin Majalisar Dokokin Amurka

Published

on

Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN) ta soki matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta ɗauka na shirin ayyana ƙungiyar a matsayin ƙungiyar ta’addanci ta hanyar gabatar da wata doka.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Baba Usman Ngelzarma, ne ya bayyana wannan suka yayin wani taron manema labarai da aka shirya a Abuja domin nuna damuwar ƙungiyar kan wannan mataki.

Shugaban ƙungiyar ya ƙi amincewa da matakin, yana mai cewa yana zubar da mutunci da kima ta wata ƙungiya ta ƙasa da aka yi wa rajista bisa doka.

Ya jaddada cewa MACBAN ba ta goyon baya, ba ta karɓa, ba ta ɓoye, ba ta ɗaukar nauyin kuɗi, kuma ba ta kare kowanne nau’in aikata laifi, tsattsauran ra’ayi ko tashin hankali a ƙasar nan. Ya ƙara da cewa ƙungiyar na ci gaba da jajircewa wajen inganta zaman lafiya da bin doka da oda a tsakanin mambobinta.

Baba Usman ya ce, a fahimtar MACBAN, irin wannan mataki daga Majalisar Dokokin Amurka zai kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, yana mai ƙara da cewa MACBAN ba ta taɓa kasancewa ƙungiyar ɗauke da makamai ko ƙungiyar tashin hankali ba.

Ya kuma tabbatar da cewa MACBAN ta yi Allah-wadai da ayyukan fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane, ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifi a Nijeriya, tare da yin Allah-wadai da su da kakkausar murya.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa MACBAN ƙungiya ce da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi wa rajista a hukumance a matsayin ƙungiyar masu samar da dabbobi da sauran masu ruwa da tsaki a sashen kiwon dabbobi.

Ya ƙara da cewa MACBAN na nan daram kan ƙudurin ta na kare haɗin kan ƙasa, bin tsarin mulki, zaman lafiya tsakanin al’umma, bunƙasa sashen kiwon dabbobi, da kuma cikakken haɗin kai da hukumomin tsaron Nijeriya wajen yaƙi da aikata laifuka.

Ya ce: “Muna roƙon Gwamnatin Tarayya cikin girmamawa da ta kare sahihai da halastattun cibiyoyin Nijeriya daga ayyana su ba bisa ƙa’ida ba a ƙasa da ƙasa, tare da tabbatar da cewa ’yan ƙasa masu bin doka da ke samar da mafi yawan sinadarin furotin na dabbobi a Nijeriya ba a wulakanta su ko cutar da tattalin arzikinsu ba.”

Ya kuma tabbatar da cewa tun daga farkon waɗannan zarge-zarge, MACBAN ta aike da wasiƙu da dama zuwa ga manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattawa da Ma’aikatar Harkokin Waje, domin neman shiga tsakani da gwamnatin Amurka.

A ƙarshe, MACBAN ta yi kira cikin girmamawa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da su ɗauki matakin doka domin kare mutunci da martabar cibiyoyin Nijeriya. Ƙungiyar ta kuma jaddada amincewarta da ƙudurin Majalisar Dokoki na kare ƙungiyoyin Nijeriya da aka yi wa rajista daga ayyana su ba bisa adalci ba a ƙasashen waje.

Cov/Bashir Mayere

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara