Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Sha Alwashin Karfafa Asun Horar Da Ma’aikata
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF.
Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa.

A cewarsa, gwamnatin jihar tana sane da muhimmancin da asusun ke da shi, musamman ga ma’aikatan da aka horas da su domin samun kwarewa a fanninsu.
Dagaceri, ya tabbatar wa shugaban asusun cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da hadin kai ga sabon ofishin na ITF da aka kafa a yankin Jigawa.

Tun da farko, Shugaban Asusun na Arewa maso Yamma, Malam Aminu Abdu ya ce sun kawo ziyarar ne a madadin babban daraktan asusun, domin nuna jin dadinsu ga Gwamna Umar Namadi bisa yadda ya samar wa sabon ofishinsu da aka kafa a yankin na Jigawa.
Aminu Abdu ya kara da cewa, asusun ya horar da ma’aikata a fadin kasar nan, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai22 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
