Kasuwanci
Gwamna Sule ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025
Gwamna Abdullahi Sule na jihar nasarawa, ya rattaba hannu a kan kasafin kudi na naira biliyan 384.3.
Gwamnan yayin da yake gabatar da kasafin kudin a gidan gwamnati, ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin kasafin ya yi yadda ya kamata.
Gwamna Abdullahi Sule ya kuma tabbatar da aniyarsa na ganin an aiwatar da tanade-tanaden kasafin kudin yadda ya kamata tare da jaddada muhimmancin samar da ingantaccen kasafin kudi wanda zai dace da abin da ake tsammani a duniya.
Ya kuma yabawa kakakin majalisar da ‘yan majalisar jiha da kwamishinoni da jami’an ma’aikatar kudi ta jiha bisa yadda suka bayar da kyakkyawar gudunmawa kan kasafin kudin.
A nasa bangaren, kakakin majalisar dokokin jihar nasarawa, Mista Danladi Jatau ya ce kudurin ya bi dokokin da suka dace kafin ya zama doka.
Ya kuma yabawa ’yan majalisa na 7 a karkashin jagorancinsa bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka.
COV/Aliyu Muraki/Lafia. Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
