Labarai
Mahukunta Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Jihar Jigawa
Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya FRCN, Dr Mohammed Bulama ya mika ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa da babban dansa.
Shugaban ya bayyana jimaminsa game da wannan babban rashi, inda ya bayyana shi a matsayin abi mai matukar raɗaɗi.

Dokta Mohammed Bulama wanda ya jagoranci wasu ma’aikatan hukumar zuwa gidan gwamnati da ke Dutse babban birnin jihar ta Jigawa, ya bukaci Gwamnan da ya mika lamuransa.

“Lalle irin wannan rashi na da radadi matuka, amma muna kara tunasar da kanmu a kullum cewa rayuwa da mutuwa suna hannun Allah SWT kuma dukkanmu muna jiran lokaci ne”.

Bulama ya yi addu’ar Allah Ya bai wa Gwamnan da iyalansa da daukacin al’ummar jihar Jigawa ikon jure wannan rashi maras misaltuwa.

Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya godewa hukumar ta Rediyon Tarayyar Najeriya bisa wannan ziyarar ta’aziyyar.
Namadi ya ce, hakan na nuni da alamar kyakyawar alakar da ke tsakanin gidan rediyon da gwamnatin jihar.

Ya ce, rasuwar mahaifiyarsa da dansa jarrabawa ce daga Allah, inda ya ce a matsayinsa na musulmi yana da yakinin cewa dukkan mai rai mamaci ne.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
