Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Farin Cikinsa Bisa Sake Farfado Da Matatar Mai Ta Warri

Published

on

 

Shugaban kasa Bola  Tinubu ya bayyana matukar farin cikinsa kan sake bude matatar mai ta Warri (WRPC) da Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya yi, yana mai bayyana hakan a matsayin wata gagarumar nasara a shekarar 2024 wanda hakan ke kara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa game da gwamnatinsa.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya sanar da cewa matatar mai ta Warri ta ci gava da aiki, makonni kadan bayan kamfanin NNPC ya  fara aikin  ganga 60,000 ta danya mai a kowace rana,a matatar mai ta Fatakwal, a watan Nuwamba.

Yayin da matatar ta Warri ta dawo aiki bayan shekaru da dama, shugaba Tinubu ya nanata kudurin gwamnatinsa na bunkasa aikin tace danyen mai da ake samu a gida Najeriya, da kuma sanya kasar a matsayin wata cibiya ta ayyukan masana’antu a Afirka.

Shugaban ya bayyana cewa tun farko gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin jam’iyyar APC ta bada kwangilar gyara matatun man kasar guda hudu.

Da yake magana game da wannan nasara, shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa karfin matatar mai ta Warri mai karfin 125,000 bpd, wanda a halin yanzu yana aiki da kashi 60 cikin 100, ya nuna gagarumin ci gaba a cikin shirin gwamnatinsa na tabbatar da ingancin makamashi da tsaro.

Shugaban ya yabawa shugaban kamfanin NNPCL Mele Kyari da tawagarsa, bisa jajircewar da suka yi na maido da martabar Najeriya a matsayin babbar kasa mai arzikin man fetur da kuma mayar da ita cibiyar tace danyen mai a Afirka.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci kamfanin NNPC da ya gaggauta aikin gyara matatar mai ta Kaduna da matatar mai mai karfin bpd 150,000 a Fatakwal, domin karfafa matsayin Najeriya a matsayin mai samar da makamashi a duniya.

Matatar mai ta Warri za ta mayar da hankali ne wajen samarwa da adana muhimman kayayyaki da suka hada daKalanzir, da iskar gas na mota, da sinadarin Naphtha, wanda zai kara habaka makamashin Najeriya da ayyukan masana’antu.

Daga Bello Wakili

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara