Labarai
Shugaban Hukumar Leken Asirin Isra’ila Ya Yi Murabus
Shugaban hukumar leken asiri ta kasar Isra’ila, Manjo-Janar Aharon Haliva, ya yi murabus saboda harin da ba a taba ganin irinsa ba da kungiyar Hamas ta kai wa kasar.
Manjo- Janar Aharon Haliva, shi ne babban hafsan soji na farko da ya yi murabus bayan caccakar da ya fuskanta kan gagarumin harin na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A takardarsa ta barin aiki, Haliva ya ce ya dauki laifin kasa dakile harin da ya sa Hamas ta tsallaka katangar Iyaka da ma duk matakan tsaron Isra’ila har ta kai harin da aka kashe mutane dubu daya da dari daya da talatin da tara, ta kuma yi awon gaba da wasu darruruwa zuwa Gaza, inda ta yi garkuwa da su.
Ana ganin hakan zai bude kofa da manyan jami’an sojin kasar za su dauki laifin harin da ake ganin Hamas ta kada hantar Isra’ila fiye da kowane lokaci.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
