Ilimi
Cibiyar Raya Albarkatun Kasa Ta Gudanar Da Taron Horaswa Na Yini 3 A Jigawa
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su hada kai don fadakar da jama’a da kungiyoyi kan mahimmancin fasahar kere-kere domin bunkasa sana’o’i.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ne ya bayyana hakan a lokacin bude horon kwanaki uku da cibiyar raya albarkatun kasa da ke Dutse, tare da hadin gwiwar wani kamfani suka shirya a Dutse.
Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana cewa, a matsayin wani sabon salo ga al’umma, ya kamata kwararru a fannin kimiyyar kere-kere su yi kokari wajen wayar da kan jama’a game da amfani da fasahar kere-kere.
Ya yi nuni da cewa, a matsayinsu na ‘yan majalisa, sun yi nazari sosai kan yadda ake amfani da fasahar kere-kere, kuma suna da ra’ayin cewa za a iya amfani da wannan fasaha a harkar noma da sauran ayyuka, kamar yadda kwararru a fannin suka bayyana.
Tun da farko, Kodinetan Cibiyar Raya Albarkatun Kasa ta Jihar Jigawa, Malam Garba Abdullahi, ya bayyana cewa an kafa cibiyar ne domin tabbatar da amfani da albarkatun da ake da su, ta hanyar amfani da ilmin halitta da fasaha wajen samar da sabbin kayayyaki, hanyoyi domin amfanin dan Adam.
Ya ce babban daraktan hukumar bincike da bunkasa fasahar kere-kere ta kasa, wanda shi ma dan asalin jihar ta Jigawa ne, ya samar da wannan cibiya, domin amfanin al’ummar jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
