Labarai
Ƙaramar Hukumar Tarauni Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Makaranta ga Sama da Ɗalibai 9,000
Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya kaddamar da rabon kayan makaranta ga sama da ɗalibai 9,000 na ajin Firamare ɗaya a makarantun firamare na gwamnati da ke faɗin ƙaramar hukumar.
An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ɗakin taro na Cibiyar Yaɗa Addinin Musulunci (Islamic Propagation Centre) da ke Tarauni.
Da yake jawabi a wajen taron, Sekure ya bayyana cewa shirin na daga cikin ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na ƙarfafa ɓangaren ilimi, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa rabon kayan makarantar na da nufin tallafa wa ƙananan ɗalibai tare da samar musu da kyakkyawan tubali na samun ingantaccen ilimi tun daga matakin farko na karatu.
A cewar Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙaramar Hukumar, Adamu Iliyasu Hotoro, shugaban ƙaramar hukumar ya jaddada cewa zuba jari a harkar ilimi na ci gaba da kasancewa muhimmin abin fifiko ga gwamnatin jihar.
Ya ƙara da cewa shirin ya yi daidai da hangen nesan Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Malam Ali Haruna Makoda, da kuma Hukumar Ilimin Firamare ta Ƙasa (SUBEB) ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Malam Yusuf Kabir, domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga dukkan yara.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su ci gaba da ƙarfafa ’ya’yansu wajen neman ilimi a kowane mataki, inda ya bayyana ilimi a matsayin muhimmin makami wajen kare matasa daga ƙalubalen munanan dabi’un zamani.
A nasa jawabin, Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kwamared Bashir Muhammad Karkasara, ya sha alwashin cikakken goyon baya da jajircewa wajen aiwatar da dukkan shirye-shiryen ilimi da gwamnatin jihar ta bullo da su.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
