Labarai
NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar
Daga Khadijah Aliyu
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da suka maƙale a ƙasashen waje, waɗanda aka dawo da su daga Niamey, Jamhuriyar Nijar, a matsayin wani ɓangare na shirin dawo da ’yan ƙasa na son rai da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa.
An kawo waɗanda aka dawo da su cikin motoci kirar bas guda 12, inda suka isa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 5 da minti 10 na yamma, inda jami’ai suka tarbe su tare da yi musu rijista da tantancewa.
Da yake magana da manema labarai a filin jirgin saman, Shugaban Ayyuka na NEMA a ofishin Kano, Dakta Nura Abdullahi, ya ce an dawo da mutanen ne bisa son ransu, ba tare da an tilasta su ba.
Abdullahi ya bayyana cewa waɗanda aka dawo da su sun haɗa da maza 267, da mata 101, sai yara maza 82, da yara mata 72, daga jihohi daban-daban ciki har da Kano, Jigawa, Filato da Bauchi.
Ya ƙara da cewa NEMA tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki sun tanadi dukkan matakan da suka dace domin kula da waɗanda aka dawo da su bayan isowarsu.
A cewarsa, da dama daga cikin waɗanda aka dawo da su sun yi hijira ne ba bisa ƙa’ida ba, domin neman ingantacciyar rayuwa, inda suka nufi ƙasashe kamar Libya da Aljeriya, amma suka bukaci dawowa gida bayan fuskantar ƙalubale a hanya.
Abdullahi ya kuma ce an tanadi wuraren zama na wucin gadi, tare da raba muhimman kayan agaji kamar abinci, bargo, gidan sauro, da kayan tsafta na mata (dignity kits) ga waɗanda aka dawo da su.
Shi a nasa jawabin, wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayya, Malam Magaji Umar, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan sauƙaƙa dawowar ’yan ƙasar cikin aminci.
Ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufofin ƙasa kan harkokin hijira, da kuma ƙudirin gwamnati na kare ’yan Najeriya a ƙasashen waje.
Umar ya ƙara da cewa wannan aiki ya samu nasara ne sakamakon haɗin gwiwar manyan hukumomi da suka haɗa da Ma’aikatar Harkokin Waje, ofisoshin jakadancin Najeriya, da Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM).
Hukumar ta NEMA ce ta tarbi waɗanda aka dawo da su tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi da suka haɗa da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA), Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira (NCFRMI), Kungiyar Red Cross ta Najeriya, da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai7 days agoGwamnatin Kano ta Samar da Babura Don Inganta Yaki da Cutar Tarin Fuka a Karkara
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
