Labarai
An Gudanar da Bukukuwan Eid-el-Fitr cikin Lumana a Kano Duk da Tsauraran Matakan Tsaro
Al’ummar Jihar Kano sun gudanar da bikin Eid-el-Fitr na bana cikin kwanciyar hankali da farin ciki, duk da tsauraran matakan tsaro da aka shimfiɗa a sassa daban-daban na birnin.
Jami’an tsaro sun bazu a muhimman wurare na birnin, ciki har da filayen sallar Idi, manyan tituna da wuraren taruwar jama’a, inda suka tabbatar da cikakken tsaro. Wannan tsari ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaito yayin gudanar da bukukuwan.
An ga yadda jama’a suka fito cikin kaya masu kyau da launuka iri-iri domin murnar kammala watan Ramadan mai alfarma. Iyali da abokai sun taru suna shagulgula, tare da yin addu’o’i da gode wa Allah bisa nasarar kammala azumi.
Har ila yau, an ga yadda aka nuna karamci da taimakon juna, inda mutane da dama suka raba abinci da makwabta, ‘yan uwa da abokai, abin da ke nuna ruhin haɗin kai da tausayi da ake danganta da bikin Sallah.
Yara kuwa sun nuna farin ciki matuƙa, sanye da sabbin kaya suna more bukukuwan. Duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, iyalai da dama sun yi ƙoƙarin samar wa ‘ya’yansu sabbin kaya, yayin da waɗanda ba su samu ba ma suka fito cikin tsafta da annashuwa.
Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da wakilinmu, ciki har da Malam Mohammad Usman da Abdullahi Fagge, sun bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana. Sun yaba da haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
A gefe guda kuma, an lura da ɗan ƙarin kuɗin sufuri a wasu sassan birnin. Duk da haka, jama’a sun ci gaba da amfani da adaidaita sahu, wato Keke Napep, da sauran motocin haya domin ziyartar ‘yan uwa da abokai.
Khadija Aliyu/Kano
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
