Labarai
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya Bukaci Musulmi Su Ci Gaba da Kyawawan Halayen Ramadan
An buƙaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da riko da darussan ruhaniya na watan Ramadan ta hanyar taimakon marasa galihu da kuma inganta zaman lafiya a cikin al’umma.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne ya yi wannan kira yayin da yake gabatar da huduba bayan jagorantar dubban jama’a sallar Eid-el-Fitr a filin Idi na Kofar Mata da ke Kano.
Sarkin ya jaddada cewa muhimmancin Ramadan ba ya tsaya ga azumi kaɗai ba, yana mai kira ga Musulmi da su rungumi halaye irin su sadaka, haƙuri da kuma ladabi da kai.
Ya kuma buƙaci muminai da su ƙara ƙaimi wajen nuna karamci da taimako ga masu buƙata, musamman marayu da marasa galihu, domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a cikin al’umma.
Hakazalika, Sarkin ya roƙi Musulmi da su ƙara yawan addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano da ma ƙasar Najeriya baki ɗaya, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da jituwa wajen ci gaban ƙasa.
Sarkin ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki ɗaya.
Dangane da harkokin noma, Muhammadu Sanusi II ya yi fatan samun kyakkyawan damina mai albarka, yana mai nuna fatan hakan zai haifar da wadataccen amfanin gona da inganta rayuwar manoma.
Haka kuma ya gargaɗi iyaye da masu kula da yara da su ƙara mai da hankali wajen tarbiyyar ‘ya’yansu, yana mai cewa kyakkyawar tarbiyya na da matuƙar muhimmanci wajen gina al’umma mai nagarta.
Daga cikin manyan baki da suka halarci filin Idi har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Sakataren Gwamnati (SSG), da sauran manyan jami’an gwamnati.
Abdullahi Jalaluddeen/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
