Connect with us

Fasaha

NBRDA Za Ta Hada Gwiwa Da KIRCT Domin Habaka Magunguna Da Yaki Da Cututtuka

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases).

Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar KIRCT  da ke Kano.

Farfesa Mustapha ya ce ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin NBRDA da KIRCT domin magance kalubalen da kasa ke fuskanta ta hanyar binciken zamani.

A matsayina na shugaba a wata muhimmiyar hukuma da ke da alhakin bincike da ci gaban fasahar halittu a fannonin abinci da noma, lafiya, masana’antu da muhalli, muna da cikakken shiri na tallafa wa KIRCT don cimma manufofinta.”

Ya yaba da kayan aiki na zamani da ke cibiyar, yana mai cewa suna da babban amfani wajen kawo sakamako mai tasiri da kuma daga martabar Najeriya a fagen binciken kimiyya na duniya.

A nasa jawabin, Daraktan Janar na KIRCT, Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana cewa cibiyar na mai da hankali kan muhimman fannoni guda uku da suka hada da taimaka wa manyan masu bincike daga Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Northwest, da  horar da sabbin masana bincike, wato masu tasuwa, da kuma kaddamar da wani shirin gwaji na horas da dalibai biyar mafi hazaka daga ajin karshe na sakandare kan ilimin fasahar halittu kafin su shiga jami’a.

Farfesa Hamisu ya jaddada muhimmancin kafafen watsa labarai da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano wajen bunkasa fasahar halittu da inganta tattalin arzikin ilimi.

Ya kuma sake nanata kudurin KIRCT na ci gaba da gudanar da bincike mai tasiri da amfani.

Wakiliyar Rediyon Najeriya ta ruwaito  cewa an kafa Kano Independent Research Centre Trust(KIRCT) ne domin gudanar da bincike kan kiwon lafiya da cututtuka masu yaduwa da wadanda ba sa yaduwa, masu matukar muhimmanci ga lafiyar jama’a a Najeriya da ma fadin nahiyar Afirka.

 

Khadijah Aliyu

 

Labarai

Ilimi15 hours ago

Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a...

Labarai2 days ago

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Daga Yusuf Zubairu Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar...

Labarai2 days ago

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Daga Khadijah Aliyu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da...

Labarai2 days ago

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar...

Labarai2 days ago

Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya

An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin...

Labarai2 days ago

Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin...

Labarai2 days ago

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka...

Labarai2 days ago

NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna

Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a...

Mafi Shahara