Labarai
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta shirya taron bita na kwanaki biyu ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara akan kara samun dabarun aiki.
Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba yace an shirya taron ne domin koyar da su dabarun sanin makamar aikin domin su fahimci tsarin mulkin tafiyar da kananan hukumomi.
Jami’in lura da kididdigar kashe kudade na shiyar Birnin Kudu Malam Usman Ya’u ya gabatar da makala kan alamuran gudanar da aiki ga kansiloli masu gafaka da masu bada shawara.
Shi ma Daraktan alamuran ma’aikata na yankin, Malam Tukur Ibrahim Doko yace taron bitar ga kansilolin masu gafaka zai kara zaburar da su akan ayyukan su.
A karshe, Malam Sani Makama da Malam Mannir Ibrahim da kuma Malam Ibrahim Muhammad sun gabatar da kasida akan kashe kudaden kananan hukumomi da kuma sanin doka da oda, da dai sauransu.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
