Connect with us

Kasuwanci

An Horas Da Mata 600 Kan Abincin Yara Mai Gina Jiki A Jigawa

Published

on

A wani yunkuri na yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma karfafa tattalin arzikin mata a jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya jagoranci bikin yaye mata 600 da suka samu horo kan yadda ake sarrafa abincin yara mai gina jiki daga kayayyakin da ake samarwa a gida, wanda aka fi sani da “Tom Brown”.

Malam Umar Namadi ya bayyana wannan shiri a matsayin wata dabara ta cikin gida da aka kirkira domin shawo kan matsalolin rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, da kuma karfafa tattalin arzikin mata.

Muna matukar godewa Allah da ya ba mu hikima da basira don kirkirar wannan tsari wanda zai taimaka mana mu cimma manufofi da dama a lokaci guda.” In ji shi.

Bayan bai wa wadanda aka horar damar samun ingantacciyar hanyar dogaro da kai, wannan kuma wata babbar dabara ce wajen yaki da rashin abinci mai gina jiki a cikin yara. Hakan kuma zai taimaka wajen hana matsalolin nakasa a kwakwalwa, domin kare damar girman yaron yadda ya dace.”

Gwamnan ya jaddada cewa Tom Brown, wanda wasu ke kira da Kwashpap, an tabbatar da ingancinsa wajen magance matsalar rashin matsakaicin abinci mai gina jiki (Moderate Acute Malnutrition – MAM) ta hanyar hadin kayan gida kamar gero, gyada da wake.

Ya kara da cewa wannan shiri na da cikakken daidaito da manufofin gwamnatin jihar na bunkasa abinci mai gina jiki, wanda ya fara haifar da sakamako mai kyau.

A cewarsa, kowace daga cikin matan 600 da suka amfana da shirin ta samu kayan fara sana’a da suka hada da injin rufe roba da kayan masarufi domin farawa da sarrafa Tom Brown a matakin gida.

Namadi ya bayyana cewa kananan hukumomi da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar za su hada gwiwa domin tabbatar da amfani da kuma shigar da wadannan kayayyaki cikin shirye-shiryen inganta abincin yara.

Ya ce, horar da wadannan mata 600 wani bangare ne na kokarin gwamnati wajen hanzarta samun ci gaba a fannin kula da rayuwar al’ummar,  da ingantacciyar lafiyar yara.

Gwamna Namadi ya kuma sake jaddada kudirin gwamnatinsa na rage dogaro da kayan abinci masu tsada da ake shigowa da su daga kasashen waje, ta hanyar bunkasa hanyoyin cikin gida masu saukin samu da kuma arha.

Ya sanar da cewa jihar Jigawa na cikin jerin jihohin da ke amfana da shirin ANRiN na Bankin Duniya, wanda ke mayar da hankali kan kara samun damar kula da lafiyayyen abinci ga mata da yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Babban burin wannan shiri shi ne kara yawan amfani da ingantattun hanyoyin kula da abinci ga mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Wannan yana da nasaba da hangenmu cewa shirin ANRiN zai taka rawar gani wajen hanzarta ci gabanmu ta bangaren samar da abinci mai gina jiki ga yara.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara