Kasuwanci
Najeriya Da Jamhuriyar Benin Za Su Karfafa Zamantakewa Da Tattalin Arziki

Ministocin harkokin wajen Najeriya, Alhaji Yusuf Tuggar da na Jamhuriyar Benin, Olushegun Adjadi Bakaru, sun gudanar da wani taro a ranar Talata, da nufin inganta harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, a mashigin Segbana da ke Jamhuriyar Benin.
Taron na tara ya kuma yi nufin dawo da mashigar tsakanin Tsamiya a Najeriya da Anguwar Sule Wara a jamhuriyar Benin zuwa rayuwa ta hanyar raya ababen more rayuwa bisa sabon fatan da shugaba Tinubu ya yi.
Ministan harkokin wajen Najeriya, ya ce taron ya samo asali ne bisa umarnin shugaba Bola Tinubu da shugaban kasar, Patrice Talon na Jamhuriyar Benin, na karfafa huldar zamantakewa da tattalin arziki tare da fadada kasuwanci tsakanin ‘yan kasashen biyu.
Ya ce, an samu ci gaba wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen yammacin Afirka a dandalin.
Shugaban hukumar kwastam na Najeriya Bashir Adewale-Adeniyi, ya ce taron na da nufin ciyar da harkokin yankin gaba tsakanin kasashen biyu da shugabannin kasashen biyu suka riga suka kirkiro.
Ya bayyana cewa, a cikin watanni shida da suka gabata, Hukumar Kwastam ta Najeriya tana aiki tare da Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Benin, wajen kara kusantar da tattalin arzikin kasashen biyu, ta hanyar tsallakawa kan iyaka cikin sauki tare da dawo da martabar kan iyakar Tsamiya da Anguwar Sule. Wara.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya godewa shugabannin kasashen biyu kan yadda suka farfado da harkokin kasuwanci da safarar kayayyaki zuwa wurare daban-daban na kasashen biyu.
Gwamnan ya jaddada cewa, jihar ta ci gaba da kyautata makwabtaka da jamhuriyar Benin kan harkokin tattalin arziki da mu’amalar al’umma a matsayin masu amfani a kan iyaka.
Romuald Wadagni, Babban Ministan Ma’aikatar Tattalin Arziki, Kudi da Hadin Gwiwa ta Jamhuriyar Benin da Mrs Adidjatou Hassan, Babban Darakta na Hukumar Kwastam ta Benin, Gwamnonin Jamhuriyar Benin da shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kebbi sun halarci taron.
COV/ABDULLAHI TUKUR/Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
