Labarai
Sarakuna Ne Tashen Hadin Kan Kasan Nan – Gwamnan JIhar Imo
Gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudancin kasar ya bukaci sarakunan yankin da su kara himma wajen tabbatar da hadin kai, ci gaba da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Gwamna Hope Uzodinma ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da sarakunan gargajiya daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Yamma suka kai masa ziyarar ban girma jim kadan bayan ganawar su a Abuja.
Gwamna Hope Uzodinma ya yi imanin cewa Iyaye Sarakuna suna da muhimmiyar gudummuwar zasu bayar wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar hada kai da Gwamnati mai ci.
Ya jaddada bukatar yin hadin gwiwa da bangaren siyasa idan har muna nufin kasar nan ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai.
Ya kara da cewa Najeriya tana da girman gaske wanda ba za ta iya mikewa da mutum daya ba, yana mai cewa idan yankin kudu ya samu hadin kan da ya dace zai yi musabaha mai kyau ga yankin Arewacin kasar nan domin ci gaban da muke nema zai zo ne kawai idan muka hada kai daga kowane bangare na kasar nan tare da rokon yin aiki tare don fahimtar bukatar hadin kan siyasa, hadewa da hadin kai wanda zai haifar da ci gaban tattalin arziki mai inganci.
Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu ya kara da imanin cewa, wannan Gwamnati a shirye take ta hada kai da Sarakuna domin ganin ta magance munanan matsalolin rashin tsaro da suka sa kasar nan gaba shekaru da dama.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnati mai ci a shirye take ta hada gwiwa da hukumomin gargajiya domin ganin kasar ta samu ci gaba, inda ya bukace su da su hada kai da gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu domin a samu dunkulewar Nijeriya, yana mai cewa a shirye yake ya daidaita kasar nan don dorewar kasa.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban tawagar, Basarake, Ooni na Ife Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya yi tsokaci sosai kan rawar da cibiyoyin gargajiya na kudancin kasar za su iya takawa wajen ganin kasar nan ta kara hade kai domin ci gaban kowa.
Ya kara da cewa Sarakunan gargajiya sun wuce siyasa ko na addini, yana mai jaddada cewa babban abin da ke damun su shi ne kasa baki daya, yana mai cewa hadin kan ya fi muhimmanci a gare su.
Sai dai ya yabawa kokarin Gwamna Hope Uzodinma na tabbatar da hadin kan kasa domin samun ci gaba mai dorewa.
Bashir Mayere/Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
