Fasaha
Masarautun Kano Zasu Gudanar da Hawan Daba A Bikin Sallah Karama

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.
Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano.
A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na zurfafa kallon al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha.
Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari wani makiya su tauye wa ‘yan kasa wannan hakki da suke da shi ba.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa dukkanin hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen samar da kariya ga jama’a a yayin bikin.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a watan Afrilun bana domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa za a sanar da ka’idojin majalisar, da sauran muhimman abubuwan da suka shafi majalisar a ranar kaddamarwar.
Ya yabawa sarakunan bisa irin balaga da kyakkyawar alaka da suka nuna tun bayan nada su, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun kwakkwarar alaka tsakanin sarakunan musamman ta fuskar matsayi.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa alakar da ke tsakaninsa da sarakunan masu daraja ta biyu abu ne na musamman.
Ya yi kira ga Gwamna Yusuf da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya don yada manufofi da tsare-tsare yadda ya kamata ga al’umma, tare da tabbatar da aiwatar da su cikin inganci.
A nasu bangaren, Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru; da mai martaba Sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir a madadin jama’arsu, sun nuna jin dadinsu ga Gwamna Yusuf bisa samar da takin zamani da samar da ababen more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da hanyoyin sadarwa a yankunansu.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27