Labarai
Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Yayi Alkawarin Inganta Tsaro

Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya sha alwashin yin aiki da gaskiya domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi.
CP Bakori ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai Kano.
CP Bakori, wanda kwanan nan ya karbi mukamin kwamishinan ‘yan sanda na 47 a jihar, ya ce daga cikin abubuwan da ya sa a gaba sun hada da magance ‘yan daba da kuma laifuka.
CP Bakori ya bayyana matsalar ‘yan daba, fadan daban, satar wayar hannu, da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Sabon Kwamishinan ya jaddada muhimmancin aikin ‘yan sandan al’umma, da nufin karfafa alaka tsakanin jami’an tsaro da jama’a.
Nadin na CP Bakori ya biyo bayan karin girma da aka yi wa magabacinsa zuwa mukamin mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG). Da dimbin gogewarsa da jajircewarsa wajen inganta tsaro, mazauna Kano za su iya sa ran samun yanayi mai aminci da tsaro a karkashin jagorancinsa.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27