Connect with us

Labarai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Ta Karɓi Ƙorafe-ƙorafe 12,446 a Shekarar 2025

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi jimillar ƙorafe-ƙorafe 12,446 daga watan Janairu zuwa Disamba na shekarar 2025.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani a Kano.

A cewarsa, daga cikin adadin ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa, shari’o’i 1,908 an sasanta su cikin lumana, yayin da 4,246 aka miƙa su gaban kotuna domin ɗaukar matakin doka.

Sheikh Mujahid ya bayyana cewa Hukumar Hisbah na ba da fifiko ga warware rikice-rikice ta hanyar sulhu (Alternative Dispute Resolution – ADR), musamman a lamuran zamantakewa da na iyali, domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a cikin al’umma.

Da yake magana kan matsalar kin ɗaukar nauyin iyali, Mataimakin Babban Kwamandan ya bayyana cewa an samu kudade har naira ₦145,406,409 da aka karɓo tare da biya domin ciyar da iyalai, ta hanyar sa hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a lokacin da ake bitar.

Ya ƙara da cewa hukumar ta gudanar da manyan ayyuka guda tara a faɗin jihar, inda ta kama mutane 132 da ake zargi, a cikin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Sheikh Mujahid ya kuma bayyana cewa bayanan da ke ofishin Hisbah sun nuna cewa mutane 93,231, maza da mata, sun ziyarci hukumar tsakanin Janairu da Disamba na shekarar 2025.

Ya shawarci al’ummar jihar da su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da jituwa, tare da ƙarfafa jama’a da su rika kai rahoton duk wani mutum ko aiki da ake zargi ga hukumomin da suka dace.

A ƙarshe, Mataimakin Babban Kwamandan ya jaddada ƙudurin Hukumar Hisbah na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa Jihar Kano ta kasance ba tare da munanan ɗabi’u na zamantakewa ba.

Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai9 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara