Labarai
Gwamnatin Kongo ta ce sojojinta ne ke iko da mafi yawan unguwannin Goma
Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya sanar da cewa yanzu haka sojojin ƙasar ne ke iko da mafi yawan unguwannin birnin Goma, da ke gabashin ƙasar.
Muhingo Nzangi, wanda shi ne ɗan majalisa mai wakiltar yankin ya shaida wa ƴan jarida cewa sojojin sun yi maganin ƴan tawayen M23 waɗanda MDD ta ce na samun goyon bayan Rwanda.
Sai dai har yanzu ƴan tawayen na iƙirarin cewa suna iko da birnin.
Wakiliyar BBC ta ce M23 na ikirarin cewa tana kokarin kare tsirarun ƴan ƙabilar Hutu ne waɗanda ake ci wa zarafi, kuma wannan lamari ne da Rwanda take goyon baya, sai dai ta ce ba ta tsoma hannu kai-tsaye cikin rikicin ba duk kuwa da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana da hannu.
Tuni dai Amurka ta yi Alla-wadai da harin da aka kai kan birnin.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
