Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta Samar da Babura Don Inganta Yaki da Cutar Tarin Fuka a Karkara

Published

on

Daga Abdullahi Jalaluddeen

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da jerin babura domin kara inganta gwajin cutar tarin fuka (TB) a yankunan karkara, a wani mataki na kokarin dakile yaduwar cutar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na bikin Ranar Yaki da Tarin Fuka ta Duniya, wadda ake gudanarwa a duk shekara a ranar 24 ga watan Maris.

Ya ce an tsara wannan shiri ne domin kai ayyukan gwaji kai tsaye zuwa yankunan da ke da wahalar isa.

A cewarsa, a halin yanzu Kano na da cibiyoyin gwaji da kula da tarin fuka guda 1,391 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya bayyana cewa sabbin baburan da aka kaddamar za su taimaka wajen cike gibin da ke akwai wajen samun damar kai ayyukan lafiya, musamman a yankunan karkara da ke nesa da cibiyoyin kiwon lafiya ko kuma inda ake fuskantar kalubalen kai dauki cikin gaggawa.

Ya jaddada cewa maganin tarin fuka, kyauta ne ga marasa lafiya tsawon watanni shida na jinya, daidai da manufar gwamnatin jihar kan yaki da cutar.

Dakta Yusuf ya kara da cewa jihar na ci gaba da samun gagarumin ci gaba wajen rage yawaitar tarin fuka da sauran cututtuka masu yaduwa da ke barazana ga lafiyar al’umma.

Kwamishinan ya sake tabbatar da kudirin gwamnati na kara karfafa tsarin sa ido kan cututtuka da kuma fadada samun muhimman ayyukan kiwon lafiya a fadin Jihar Kano.

Labarai

Ilimi13 hours ago

Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a...

Labarai2 days ago

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Daga Yusuf Zubairu Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar...

Labarai2 days ago

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Daga Khadijah Aliyu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da...

Labarai2 days ago

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar...

Labarai2 days ago

Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya

An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin...

Labarai2 days ago

Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin...

Labarai2 days ago

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka...

Labarai2 days ago

NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna

Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a...

Mafi Shahara