Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Farfado da Cibiyoyin Kiwon Dabbobi a Gumel, Birniwa da Kazaure
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware sama da naira biliyan 17 domin bunƙasa harkar kiwo a faɗin jihar.
Kwamishinan Harkokin Kiwon Dabbobi na jihar, Farfesa Abdulrahman Salim ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin kuɗin da ma’aikatarsa ta gabatar na shekarar 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai kula da harkokin noma, a Dutse.
Farfesa Abdulrahman Salim ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen aiwatar da manyan ayyuka daban-daban da suka shafi bunƙasa kiwo a shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa ma’aikatar ta shirya kafa wuraren kiwo (ranches) a sassan jihar, inda makiyaya da sauran masu kiwon dabbobi za su zauna.
A cewarsa, a waɗannan wuraren da za a ware domin kiwo, makiyaya za su samu ingantaccen abincin dabbobi, makarantu masu kyau ga ’ya’yansu, cibiyoyin lafiya, asibitocin dabbobi, kasuwanni, wutar lantarki da ruwan sha.
Farfesa Salim ya ce hakan zai taimaka wa ma’aikatar wajen rage yawan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a kuma yi amfani da kuɗin wajen kafa asibitocin dabbobi a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar, da asibitocin dabbobi na shiyyoyi guda bakwai, tare da babban asibitin dabbobi na tsakiya da zai zama cibiyar tura marasa lafiya (referral centre).
Ya ce duk da suna da ƙwararrun likitocin dabbobi, akwai buƙatar horaswa da sake horas da ma’aikatan matsakaici da na ƙananan matakai.
Haka kuma ya bayyana cewa ma’aikatar ta shirya farfaɗo da cibiyoyin kiwon dabbobi guda uku da ke Gumel, Birniwa da ƙaramar hukumar Kazaure, inda ya ce tuni aka fara aiki a wasu daga cikin cibiyoyin.
Farfesa Salim ya ƙara da cewa za a fara ne da kafa wuraren kiwo guda uku a matsayin gwaji, tare da ƙanana da za a danganta da sarrafa kayan madara ko kayan kiwon dabbobi na makiyaya.
Ya ce ma’aikatar na da ayyuka masu yawa a fannin sarrafa nama, inda aka raba su kashi biyu. Na farko shi ne ayyukan mazabun ’yan majalisar dokoki da suka kai kimanin naira miliyan 355, waɗanda suka haɗa da gina wuraren yanka dabbobi da manyan gidajen yanka.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
