Connect with us

Fasaha

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da nufin magance matsalolin da suka shafi ci gaban Jami’ar.

 

A wata sanarwa da shugaban Kungiyar Sa’idu Isa Abubakar ya sanya wa hannu, ta ce Jami’ar tana gudanar da ayyukanta ba tare da Majalisar Gudanarwa ba, tun bayan rushewar da gwamnatin mai ci ta yi.

 

Sanarwar ta lura cewa sake fasalin majalisar gudanarwar shi ne mabuɗin don samar da aiki mai inganci tare da jaddada cewa Majalisar Mulki tana taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawara, ɗaukar ma’aikata, gudanarwa, Taro da sauransu.

 

Sanarwar ta kuma nemi a biya kudaden alawus din karatun da aka samu na tsawon zango zama biyar daga shekara ta 2022.

 

Sanarwar ta kuma kara tunatar da gwamnatin Sokoto bukatar ta cire kudaden da kungiyoyin hadin gwiwa suka yi na cirewa da kuma biyan kudaden da ake bin su tare da jaddada cewa ma’aikatar kudi ta jiha ce ta cire kudaden daga albashin ‘ya’yan kungiyar kuma ba a tura kudaden zuwa asusun kungiyar ba.

 

A cewar sanarwar, sauran abubuwan da suka dame su sun hada da kafa dokar karin albashi, aiwatar da bayar da kyautar albashi da kuma kammala rukunin gidajen ma’aikatan jami’ar.

 

Sanarwar ta yi nuni da cewa, wadannan bukatu za su tabbatar da gudanar da ayyukan Jami’ar yadda ya kamata da kuma jin dadin mambobin.

 

NASIR MALALI/Wababe

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara