Labarai
Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.
A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.
Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:
- Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza
- Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu”
- Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba
Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:
- Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Sakin duka sauran Isra’ilawan da take riƙe da su
- Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba
- Miƙa duka makamanta
BBC/Hausa
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
