Labarai
Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Kenya Sun Karu
Kungiyar likitoci ta Kenya ta ce adadin wadanda suka mutu, sanadiyar zanga-zangar karin kudin hajari da gwamnatin kasar ta sanar, ya karu zuwa 13.
Shugaban kungiyar Simon Kigondu ne ya tabbatar da adadin wata zantawa da ya yi da manema labarai a yau Laraba.
Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu matasa ne, sun mamaye zauren majalisar dokokin kasar a jiya Talata, inda suka rika jifar ‘yan sanda da duwatsu da kuma rushe shingen jami’an tsaro don kutsa kai cikin harabar majalisar.
Bayan faruwar lamarin, shugaban kasar William Ruto ya tura da jami’an soji don tarwatsa masu zanga-zangar.
Shugaba Ruto ya lashi takobin daukar tsauraran matakai don tabbatar da zaman lafiya a kasar, inda ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.
Sai dai duk da daukar wancan mataki, masu zanga-zangar sun ce babu gudu babu ja da baya game da kudirinsu na ci gaba da zanga-zangar, har sai hakarsu ta cimma ruwa.
Wani jami’i a asibitin Kenyatta da ke birnin Nairobi, ya ce a asibitin kadai, jami’ansu sun duba mutane 160 da suka samu raunukan harhasai, wasu kuma kananan raunuka.
Ɗaya daga cikin abubuwan da masu zanga-zangar ke bukata shi ne shugaban kasar William Ruto ya sauka daga mukaminsa.
Matasan sun bayyana matakin gwamnatin Ruto na lafta wa jama’a haraji a matsayin wani sabon yunƙuri na jefa al’umma cikin ƙarin musiba, ganin yadda tuni matsalar tsadar rayuwa ta yi musu dabaibayi.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
