Connect with us

Labarai

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Published

on

Daga Khadijah Aliyu

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da suka maƙale a ƙasashen waje, waɗanda aka dawo da su daga Niamey, Jamhuriyar Nijar, a matsayin wani ɓangare na shirin dawo da ’yan ƙasa na son rai da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa.

An kawo waɗanda aka dawo da su cikin motoci kirar bas guda 12, inda suka isa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 5 da minti 10 na yamma, inda jami’ai suka tarbe su tare da yi musu rijista da tantancewa.

Da yake magana da manema labarai a filin jirgin saman, Shugaban Ayyuka na NEMA a ofishin Kano, Dakta Nura Abdullahi, ya ce an dawo da mutanen ne bisa son ransu, ba tare da an tilasta su ba.

Abdullahi ya bayyana cewa waɗanda aka dawo da su sun haɗa da  maza 267, da mata 101, sai yara maza 82, da yara mata 72, daga jihohi daban-daban ciki har da Kano, Jigawa, Filato da Bauchi.

Ya ƙara da cewa NEMA tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki sun tanadi dukkan matakan da suka dace domin kula da waɗanda aka dawo da su bayan isowarsu.

A cewarsa, da dama daga cikin waɗanda aka dawo da su sun yi hijira ne ba bisa ƙa’ida ba, domin neman ingantacciyar rayuwa, inda suka nufi ƙasashe kamar Libya da Aljeriya, amma suka bukaci dawowa  gida bayan fuskantar ƙalubale a hanya.

Abdullahi ya kuma ce an tanadi wuraren zama na wucin gadi, tare da raba muhimman kayan agaji kamar abinci, bargo, gidan sauro, da kayan tsafta  na mata (dignity kits) ga waɗanda aka dawo da su.

Shi a nasa jawabin, wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayya, Malam Magaji Umar, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan sauƙaƙa dawowar ’yan ƙasar cikin aminci.

Ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufofin ƙasa kan harkokin hijira, da kuma ƙudirin gwamnati na kare ’yan Najeriya a ƙasashen waje.

Umar ya ƙara da cewa wannan aiki ya samu nasara ne sakamakon haɗin gwiwar manyan hukumomi da suka haɗa da Ma’aikatar Harkokin Waje, ofisoshin jakadancin Najeriya, da Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM).

Hukumar ta NEMA  ce ta tarbi waɗanda aka dawo da su  tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi da suka haɗa da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA), Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira (NCFRMI), Kungiyar Red Cross ta Najeriya, da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara