Ilimi
Jami’ar Bayero Ta Kori Dalibai 171 Bisa Gabatar da Takardun Bogi
Daga Khadijah Aliyu
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta amince da korar dalibai 171 bisa laifin gabatar da takardun shigar jami’a na bogi.
An yanke wannan hukunci ne a yayin taron majalisar jami’ar karo na 433, bayan rahoton kwamitin majalisar kan matsalolin rashin sahihancin takardun shiga jami’ar.
A cewar wata sanarwa da jami’ar ta fitar a cikin mujallarta ta mako-mako, an gano cewa daliban da abin ya shafa sun gabatar da takardun bogi yayin neman gurbin karatu, wanda ya saba wa dokokin jami’ar.
Jami’ar ta bayyana cewa wannan laifi ya saba wa Sashe na 20.7, rukuni na A (vii) na dokokin jarabawa da harkokin ilimi, wanda ke tanadin hukuncin kora ga irin wannan laifi.
BUK ta kara da cewa daliban da abin ya shafa sun fito ne daga sassa da matakai daban-daban, tare da jaddada cewa matakin na daga cikin kokarin tsaftace harkar karatu da kuma kare martabar jami’ar.
A wani bangare kuma, majalisar ta amince da korar Yusuf Muhammad Sani, dalibi a sashen Injiniyan Gine-gine, bisa zargin hannu a dukan masu sanya ido a jarabawa.
Jami’ar ta ce lamarin ya kawo tsaiko a gudanar da jarabawar tare da karya dokokin ladabtar da dalibai.
Hukumar jami’ar ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya da nagarta a harkokin ilimi, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya dokokinta zai fuskanci tsattsauran hukunci.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
