Connect with us

Labarai

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Published

on

Daga Aminu Dalhatu 

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa kokarinsu na hadin gwiwa wajen samun nasarar rabon kayan abinci na watan Ramadan a kananan hukumomi 14 na jihar, domin tallafa wa marasa galihu da marayu.

Ta yi wannan yabon ne a lokacin rabon kayan a karamar hukumar Gusau, inda ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin rage radadin rayuwa ga iyalai a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

A cewarta,  rabon ya shafi dukkan kananan hukumomin jihar, inda aka fara daga Shinkafi da Zurmi, sannan Birnin Magaji da Kaura Namoda, daga nan sai Gummi da Bukkuyum, Anka da Talata Mafara, Maradun da Bakura, Maru da Bungudu, sannan aka kammala a Tsafe da Gusau.

Hajiya Huriyya ta bayyana cewa an samu nasarar raba kunshin kayan abinci guda 50,000 a fadin jihar. Ta ce kowane kashi ya kunshi buhun shinkafa mai nauyin kilo 20, wake, masara da gero, da kilo 5 na sukari, taliya, man girki, gishiri, da kuma sutura ga mata.

Uwargidan gwamnan ta kuma bayyana cewa an kafa kwamitoci a matakin gunduma domin yin aiki tare da shugabannin kananan hukumomi, don tabbatar da adalci, gaskiya da rikon amana wajen rabon kayan.

Mun umurci kwamitocin da su gudanar da aikinsu da gaskiya, rikon amana da tsoron Allah, domin sauje amanar da aka dora musu ce,” in ji ta.

Ta kuma gode wa mambobin tawagarta da suka hada da direbobi, jami’an tsaro, daraktocin Zakka da ma’aikatansu, ‘yan jarida, masu aikin sa kai da duk wadanda suka bada gudunmawa wajen samun nasarar shirin.

Kun nuna jajircewa da sadaukarwa. Allah ne kadai zai saka wa kowa.” in ji ta.

Hajiya Huriyya ta kuma yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa goyon bayansa da jajircewarsa wajen inganta jin dadin al’ummar jihar, tare da sauran masu taimako da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar shirin.

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara