Ilimi
Jami’ar Abdulkadir Kure Tana Daya Daga Cikin Jami’o’in Ci gaban Kasa – VC
Shugaban jami’ar Abdulkadir Kure da ke jihar Neja, Farfesa Mohammed Aliyu Paiko ya bayyana cewa jami’ar na daya daga cikin jami’o’in da ke bunkasa cikin sauri a Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Neja a ofishinsa da ke Minna.
Farfesa Aliyu Paiko ya bayyana cewa jami’ar da ta fara daukar dalibai kusan 100 a shekarar 2024 a yanzu haka tana da dalibai sama da 700 domin a cewarsa karin dalibai suna kan aikin rijistar ne saboda jami’ar tana dada daukaka.
Shugaban jami’ar ya ci gaba da bayyana cewa, bisa ga manufar fadada jami’ar, sama da dalibai 3,500 ne suka rigaya suka mika takardar neman gurbin karatu na shekarar 2025/2026 yana mai jaddada cewa jami’ar ta riga ta zama cibiyar kasuwanci a dukkan fannoni musamman a fannin ilimi na musamman.
Sai dai ya bayyana cewa ta hanyar Abdulkadir Kure Center for Basic and Professional Studies da GreenTech ICT Hub Initiative, an bude jami’ar ne domin hadin gwiwa da kwararru musamman ma’aikatan yada labarai.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Abu Nmodu ya bayyana cewa makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin biyu ke da shi.
Kwamared Abu Nmodu wanda ya jaddada rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen fadakarwa, ilmantar da jama’a da kuma nishadantar da jama’a, ya sanar da Shugaban kungiyar cewa NUJ na gudanar da kwasa-kwasan ilimi kan harkokin yada labarai da aikin jarida a karkashin cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa (IIJ) a dakin taro na IBB Pen House da ke Minna.
Shugaban kungiyar ta NUJ ya bada tabbacin Shugaban jami’ar da hukumar gudanarwar jami’ar na ci gaba da bayar da goyon baya domin baiwa kungiyar damar cimma burin da ta sa a gaba.
ALIYU LAWAL.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
