Ilimi
Daliban Jami’ar Nasarawa 3 Sun Mutu A Tirmitsitsin Rabon Tallafi
Daliban Jami’ar Jihar Nasarawa 3 ne ake fargabar sun mutu sakamakon turmutsitsin da ya faru a lokacin rabon tallafin shinkafa da gwamnatin jihar ta bada a yau Juma’a a garin Keffi.
Lamarin ya faru ne a dandalin taro na makarantar inda aka ajiye buhunan shinkafa ana jiran isowar gwamna Abdullahi Sule domin fara rabon kayayyakin.
A cewar wani dalibin da lamarin ya faru a gaban idonsa, Moses Ajah, ya ce gungun daliban da ke dakon shiga dandalin sun ci karfin jami’an tsaro tare kutsawa dandalin taron.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka.
Ya ce wasu dalibai sun kwashi buhunan shinkafan suka gudu da su duk da cewa Gwamnan bai kai ga iiowa wurin ba domin kaddamar da rabon.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ga jami’an ‘yan sanda suna bin daliban dakunan kwanansu don kwato buhunan shinkafar da suka yi awan gaba da su.
Da aka tuntubi jami’in yada labarai da kula da jami’ar, Mista Abraham Ekpo, ya ce yana sane da lamarin amma har yanzu bai samu cikakken bayani a kai ba.
Aliyu Muraki
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
