Ilimi
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyoyin Bada Abincin Buda Baki A Manyan Makarantu
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa cibiyoyin bada abincin buda baki a manyan makarantun jihar guda 10, domin tallafa wa dalibai a lokacin azumi.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati na Dutse.
A cewarsa, gwamnatin jihar na shirin ciyar da mutane sama da miliyan uku da dubu dari takwas a watan Ramadan na bana domin tallafawa gajiyayyu da marasa galihu.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta amince da naira kusan miliyan dubu dari uku domin ciyar a watan Ramadan a cibiyoyi 609 da aka kafa a fadin jihar.
Ya ce shirin tallafin da aka tsara ya yi daidai da manufofin gwamnati na rage wahalhalu ga marasa galihu musamman a wannan lokaci na da ake ciki.
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da kafa kwamitin wucin gadi a dukkanin kananan hukumomi 27, wanda kwamishinan kananan hukumomi ko kuma manyan mashawarta na musamman a kananan hukumomin za su jagoranta domin tabbatar da gaskiya.
Sagir Musa ya ce, sauran mambobin kwamitin sun hada da ‘yan majalisar dokokin jihar, mataimaka na musamman, shugabannin kananan hukumomi da DPO na ‘yan sanda.
Sauran sun hada da jami’in tsaro na DSS na karamar hukumar, wakilin hakimai, da sakataren karamar hukuma wanda zai zama sakataren kwamitin.
Hakazalika majalisar ta kuma amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan 125 don ƙarin siyan kayan abinci da za a raba ga marasa galihu, a ƙoƙarin da ake yi na rage wahalhalun rayuwa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
