Labarai
Gobara Ta Hallaka Mutane Arba’in Da Daya A Kuwait
Wata gobara da ta tashi a wani gidan ma’aikata da ke garin Mangaf na kasar Kuwait, ta hallaka mutane 41, kamar yadda mataimakin firai ministan kasar Sheikh Fahad Yusuf Saud Al-Sabah ya tabbatar.
Cikin wani jawabi da mataimakin firai ministan ya yi, ya ce gidan matattara ce ta mutane da ke kananan ayyuka a kasar, wanda mafi akasarin su bakaken fata ne.
Sheikh Al-Sabah ya alakanta tashin gobarar da tsantsar son zuciya da kuma rashin bin ka’ida da wasu dillalan da ke bada gidajen haya ke nunawa.
Bayanai sun ce wutar ta tashi da misalin karfe 6 na safiyar Laraba agogon kasar, kamar yadda Manjo Janar Eid Rasheed Hamad daya daga cikin mahukuntan kasar ya tabbatar.
Ya ce an yin nasarar ceto wasu da dama, yayin da wasu suka gamu da munanan raunuka, sai dai kuma abin tashin hankalin shi ne yadda wutar ta kona mutane 41 kurmus.
Manjo janar Rasheed ya ce kowanne lokaci hukuma na iya bakin kokarinta wajen ganin ta rage cinkoso a irin wadannan gidaje, amma masu bada haya sai su yi amfani da barauniyar hanya wajen tara mutane kawai don neman kudi.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar sai dai jami’ai na ci gaba da bincike.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
