Labarai
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Ta Yi Wawan Kamu
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka shafi ‘yan fashi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sufurtandan Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce an samu nasarar kame mutanen ne ta hanyar sintiri da kuma tattara bayanan sirri.
Kiyawa ya bayyana cewa, kayyakin da aka gano sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, bindigarsamfurin harbi ka ruga daya, bindiga kirar famfo guda daya, alburusai 26, harsashi masu rai guda 17, motoci guda biyu, raguna 16, da sauran muggan makamai da na fasa gidaje.
“Ana ci gaba da bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.”
Ya yi nuni da cewa Kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
