Labarai
Ana Cigaba Da Ceto Mutanen Da Suka Makale Wajen Hakar Ma’adanai A Naija
Masu aikin ceto sun ceto mutane bakwai da suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Ministan ma’adanai, Dele Alake ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar ranar Talata a Abuja.
Ya ce an tura masu bayar da agaji zuwa wajen da lamarin ya faru, inda ya kara da cewa ana aikin ceton tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa kimanin mutane 30 ne suke makale cikin ramin da ake hakar ma’adanai da wani ke aiki.

Kamfanin dillancin labaran na NAN ya kara da cewa Darakta-Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Neja (NSEMA)Alhaji Abdullahi Arah ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.
Ministan ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ya nuna yadda ta himmatu wajen ganin an dakile asarar rayuka, da kuma ceto wadanda suka makale.
“Da samun labarin faruwar lamarin, sai muka tura jami’an kula da ma’adanai na tarayya (FMO) da jami’an hukumar binciken ma’adanai wajen domin ceto wadanda suka makale“.
“Tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai, mun ceto mutane bakwai da suka makale, ana kuma ci gaba da gudanar da aikin ceto a wajen,” in ji shi.
Ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar yin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
