Labarai
Najeriya Ta Ki Amincewa Da Sake Fasalin Siyasa Da Tsaro Na Kungiyar AU
Najeriya ta nuna adawa da wani yunkuri na sake fasalin Sashen Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) (PAPS), saboda damuwa game sanadin da ka iya tabarbarewar hanyoyin zaman lafiya da siyasa na kungiyar.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da wannan matsayi a madadin Shugaba Bola Tinubu, a lokacin da ake tattaunawa kan ssauye-sauyen kungiyar AU.
Shugaban na Najeriya ya kuma yabawa shugabanin kasashen Ruwanda Paul Kagame da William Ruto na Kenya, bisa shawarwarin da suka gabatar na kawo sauyi da nufin ganin kungiyar ta AU ta kara zage damtse wajen magance matsalolin mambobin kungiyar.
Shugaba Tinubu ya bayyana goyon bayansa na samar da kwamitin sa ido kan shugabannin kasa da na gwamnati, wanda shugaba Ruto zai jagoranta, domin sa ido kan sauye-sauyen kungiyar ta AU.
Bugu da kari, ya amince da kudirin takaita ajandar taron kolin kungiyar AU zuwa wasu muhimman abubuwa uku.
Sai dai Tinubu ya ki amincewa da kudirin raba sashen na PAPS, wanda a halin yanzu jami’in diflomasiyyar Najeriya Ambasada Bankole Adeoye ke jagoranta, wanda a kwanan nan aka sake zabensa a karo na 2.
Tinubu ya bayar da hujjar cewa shirin sake fasalin zai haifar da kashe kudade na babu-gaira-babu dalili, da kuma kawo cikas ga wasu ayyukan da aka sa a gaba.
A yayin da yake jaddada gaskiya da kuma hada kai, Tinubu ya yi kira da a dauki matakin yin garambawul ga manufofin kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU. “Ya kamata mu maida hankali ne kan wuraren da aka riga aka cimma matsaya, maimakon kokarin kara tunkarar wasu sabbin abubuwa.” In ji shi.
Najeriya ta yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ga sauye-sauyen kungiyar ta AU ba tare da bata wani lokaci ba, muddin dai sun kasance bisa gaskiya.
Daga Bello Wakili
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
