Labarai
Kwara NUJ Iftar: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Rika Tsayawa Kan Gaskiya
An bukaci ‘yan jarida su tabbatar rahotanninsu sun dogara da gaskiya tare da guje wa son zuciya domin kare mutuncinsu a gaban Allah.
Kwamishinan Ilimi da Bunƙasa Jarin Dan Adam na jihar Kwara, Dr. Lawal Olohungbebe, ne ya bayyana hakan a wajen bikin buda baki na shekara-shekara na Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Kwara na 2026 da aka gudanar a Ilorin.
Taron wanda ke dauke da taken “Shugabanci, Kafafen Yada Labarai da Yaki da Rashin Tsaro a Al’umma”, ya mayar da hankali kan rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen inganta zaman lafiya.
Dr. Olohungbebe ya jaddada cewa ya zama wajibi ‘yan jarida, musamman Musulmi, su rika tabbatar da gaskiya da tantance bayanai kafin wallafa su, musamman a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro.
Ya ce addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin tabbatar da sahihancin labari kafin yada shi, yana mai bayanin cewa Alkur’ani ya umarci muminai su binciki gaskiyar duk wani bayani kafin yada shi domin kauce wa yaudarar jama’a.
Kwamishinan ya kara da cewa jita-jita da bayanan karya ba sabon abu ba ne, domin sun kasance tun a zamanin Annabi Muhammad (SAW) lokacin da hanyoyin sadarwa suka takaita ga magana kai tsaye ko kuma wasiku.
Ya kuma gargadi ‘yan jarida da su yi la’akari da illar da wasu rahotanni ka iya haifarwa ga zaman lafiya da tsaron al’umma, tare da jaddada cewa malamai ma suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
A nata jawabin, Kwamishinar Raya Al’umma ta jihar Kwara, Dr. Maryam Imam, ta yaba wa kungiyar NUJ ta jihar bisa shirya wannan taro.
Ta ce taron ya bai wa mambobin kungiyar damar samun karin karfafa imaninsu a watan Ramadan, tare da karfafa musu gwiwa su ci gaba da riko da kwarewa da kyawawan dabi’u a aikinsu.
Shi ma a jawabinsa, Shugaban NUJ na jihar Kwara, Malam Lanre Ahmed, ya ce yayin da aikin sojoji shi ne kare iyakokin kasa, su kuma ‘yan jarida na da alhakin tabbatar da rahotanninsu ba su ba masu aikata tashin hankali wata dama ko karin daukaka.
Ya kuma nuna damuwa kan abin da ya kira gasa marar amfani tsakanin wasu malaman addini wajen neman daukaka, yana mai cewa ya kamata shugabannin addini su kasance abin koyi ga al’umma.
Malam Ahmed ya shawarci kafafen yada labarai da su guji yada irin wadannan sabani, maimakon haka su mayar da hankali kan batutuwan da ke karfafa hadin kai da kyawawan dabi’u.
A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Lafiya da Gina Jiki na Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Seun Ogunniyi, ya bukaci ‘yan jarida su yi nazari kan darasin da bakon malamin taron ya gabatar.
Ya ce ya zama wajibi ‘yan jarida su rika tacewa da tantance labarai kafin yada su, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta aikin jarida mai nagarta.
A karshe, Shugabar Kwamitin Shirya Iftar na NUJ na 2026 a jihar Kwara, Binta Abubakar Mora, ta gode wa bakon malamin bisa gabatar da muhimmin darasi da ya ba mahalarta jagoranci na ruhaniya a lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro.
Ta ce darasin ya kuma haskaka muhimmiyar rawar da ‘yan jarida za su taka wajen taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro a kasa.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai6 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai6 days agoTinubu Ya Nada Lamido Yuguda Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa
-
Labarai6 days agoKwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoJami’ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi
-
Labarai4 days agoKwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara
-
Labarai4 days agoAn Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya
-
Labarai4 days agoMatashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba
-
Labarai1 day agoJIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah
