Connect with us

Labarai

JIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah

Published

on

Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Ash Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bukaci Gwamnan jihar Niger, Umar Bago, da ya gaggauta sanya hannu kan dokar Hisbah da Majalisar Dokokin jihar ta amince da ita kwanan nan.

Sai dai Sheikh Jingir ya gargadi gwamnan da kada a mayar da batun dokar Hisbah zuwa siyasa, yana mai cewa dokar an tanade ta ne domin Musulmi, musamman ganin cewa kusan kashi 95 cikin 100 na al’ummar jihar Niger Musulmi ne.

Malamin ya bayyana hakan ne a wajen rufe tafsirin watan Ramadan na bana da aka gudanar a harabar gidan marigayi Malam Ladan a Minna, babban birnin jihar.

Ya jaddada cewa dokar Hisbah na inganta adalci, daidaito da gaskiya kamar yadda koyarwar addinin Musulunci ta tanada.

An wakilci Sheikh Jingir ne da Dr. Aliyu Ibrahim Shafi’i daga karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi, wanda ya jagoranci tafsirin na shekara-shekara. Ya kuma kwantar wa wasu Kiristoci da ke nuna damuwa hankali, yana mai cewa a wasu lokuta har wasu ‘yan kabilar Igbo a jihar Bauchi kan kai kararrakinsu, har ma da matsalolin aure, gaban hukumar Hisbah domin a sasanta musu.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS reshen jihar Niger, Sheikh Abubakar Abu Sumayyah, wanda Ustaz Muhammad Gulbin Sunnah ya wakilta, ya bayyana cewa dokar Hisbah ba wai domin cutar da kowa ba ce, yana mai kira ga jama’a su bayar da hadin kai domin ganin gwamnan ya sanya hannu a kanta cikin gaggawa.

Shi ma Shugaban Kwamitin Tafsir, Alhaji Ibrahim Dumus, wanda Alhaji Salisu Musa Koko ya wakilta, ya yaba wa tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida mai ritaya da kuma tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar bisa goyon bayan da suka bayar ga tafsirin.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin na shirin fara biyan kudin makaranta ga wasu marayu a makarantun firamare da sakandare a kananan hukumomin Bosso da Chanchaga na jihar.

A yayin taron, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Chanchaga, Malam Abdu Buba, ya bayar da gudunmawar naira miliyan daya, yayin da Shugaban karamar hukumar Chanchaga, Dr. Mustapha Jibrin Alheri, ya bayar da naira dubu dari biyar domin tallafa wa ayyukan kwamitin tafsirin.

Aliyu Lawal/Minna

Labarai

Labarai14 hours ago

Gidauniyar NASARA Ta Raba Kayayyakin Ramadan da na Sallah ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Marayu da zawarawa sama da dubu ɗaya ne suka amfana da tallafin kayayyakin Ramadana da na Sallah...

Labarai18 hours ago

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Taiwo Oyedele Ministan Kudi

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin  Minista a Ma’aikatar. An gudanar...

Labarai22 hours ago

Yi Wa Shuwagabanni Biyayya Ne Zai Kai mu Ga Ci Gaba – Garkuwan Kudun Zazzau

Dokta Muhammad Sani Uwaisu FCNA, Garkuwan Kudun Zazzau, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmin Duniya baki daya da su...

Labarai23 hours ago

Gwamnatin Zamfara Ta Amince da Biyan Albashin Watan Maris Gabanin Bukukuwan Karamar Sallah

Daga Aminu Dalhatu Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da...

Labarai1 day ago

Mambobin APC Sun Kai 158,697 a Zamfara Bayan Sauya Shekar Gwamna Lawal

Adadin mambobin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya karu zuwa 158,697, kwanaki uku kacal bayan sake bude tsarin rajistar mambobi...

Labarai1 day ago

Kwara NUJ Iftar: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Rika Tsayawa Kan Gaskiya

An bukaci ‘yan jarida su tabbatar rahotanninsu sun dogara da gaskiya tare da guje wa son zuciya domin kare mutuncinsu...

Labarai1 day ago

‘Yan Sanda Sun Bankado Maboyar Masu Garkuwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da...

Labarai1 day ago

JIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah

Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Ash Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya...

Labarai4 days ago

An Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya

Jami’an kula da hanya na Hukumar Kiayyae hadura ta kasa a Jos sun samu damar yin gwajin idanu da kuma...

Labarai4 days ago

Kwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara

Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Jihar Kwara, ta ce ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta da kuma...

Mafi Shahara