Labarai
Jami’an Gwamnatin Tarayya Sun Isa Saudiyya Wajen Jana’izar Aminu Dantata
Wata tawagar gwamnatin tarayyar ta isa kasar Saudiyya domin karbar gawar marigayi dattijon dan kasuwa kuma dan kishin kasa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, gabanin jana’izar sa a birnin Madina.
Alhaji Dantata, wanda ya rasu a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, yana da shekaru 94 a duniya, ya samu karbuwa sosai saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen harkokin kasuwanci, da taimakon jama’a da kuma ci gaban kasa.
A cewar wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ya fitar, tawagar ta Najeriyar ta bar kasar ne a ranar Lahadin inda suka isa birnin Madina da sanyin safiyar Litinin domin halartar jana’izar.
Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ke jagorantar wannan ayarin Gwamnatin Tarayya.
Sauran mambobin sun hada da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnai, Prince Lateef Fagbemi, SAN; da Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris; da kuma ministan kasa a ma’aikatar gidaje, Honorabul Yusuf Abdullahi Ata.
Haka kuma a cikin tawagar akwai fitattun malaman addinin musulunci da suka hada da Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Khalifa Abdullahi Muhammad limamin masallacin Dantata dake Abuja. Har ila yau, jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke Jeddah, karkashin jagorancin Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya, sun bi sahun tawagar tare da gudanar da shirye-shiryen jana’izar da za a yi a yau (Litinin) a birnin Madina.
Sanarwar ta bayyana cewa, Alhaji Aminu Dantata shahararren dan kasuwa wanda aka sheda da rikon amana, da yi wa kasa hidima wanda ya dauki tsawon shekaru da dama yana shafar rayuka da dama a fadin Najeriya da ma sauran wurare.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
